Shin Masu Mulki A Nijeriya na Tausayin Talakawansu kuwa? Daga Kais Daud Sallau

0

Ba shakka tausayin mai mulki akan wandanda yake mulka abu ne wanda ya ke da mahimmanci a shugabanci. Shugaba nagari, mai imani ne ake samun shi da irin wannan tausayin.

Duk lokacin da ake ce an samu shugaba wanda ya ke da tausayin wadanda ya ke mulka, toh ba shakka a ko da yaushe burinsa yaga yaya zai kyautatawa wadanda ya ke mulka ne ba biyan bukatan kanshi ba.

Duk lokacin da shugaba ya zama mai tausayawa al’ummarsa ne, toh zaka ga ya shiga zuciyar mutanen shi, kuma duk alkawarin da yayi musu, suna sa rai zai cika saboda yarda da suka bashi.

Amma a duk lokacin da aka ce shugaba ya zama mara tausayi da son zuciya, toh wannan shugaban duk halin da al’ummarsa zasu shiga idan har wannan abin ba zai bata mulkin shi ba, toh shi ba ruwan shi. Duk lokacin da yayi alkawari bazai cika ba. Toh wannan shugaban baya samun karbuwa a gurin al’ummar da ya ke mulka. Kuma duk lokacin da yayi wani alkawari, ba za su yarda ba, domin kallo makaryaci su ke yi mishi. Irin wadannan shugabannin kansu kawai suka sani da yaransu.

Shin Masu Mulki a Najeriya Suna Tausayawa Talakawansu?

Babu shakka akasarin masu mulki a Najeriya ba talaka ba ne a gabansu, ba su tausayin talaka, ba su so suma ga talaka a inda suke. Duk da cewa talakawa suke kaisu wannan matsayin, amma daga lokacin da suka hau karagar mulki, toh sun sallame talakawan kenan, sai zabe ya sake juyowa. Locacin kuma talaka na da amfani a gurinsu.

Ta inda zaka ga gane cewa talaka ba shi bane a gaban akasarin masu mulki a Najeriya shi ne, dubi harkan ilmi a kasannan, wallahi kullum kara kudin makaranta suke yi, suna son su kai matsayin da dan talaka ba zai iya zuwa makaranta ba saboda tsada, hankalinsu a tashe yake saboda yanzun yaran talakawa suna samun daman yin karatu, suna fahimtar mai akeyi a gwamnati, suna fahimtar duk iri zaluncin da masu mulkin ke yiwa talakawa. Su kuma karatun da yaran talakawan suke yi ne basu so, sunfi son yaran talakawan su zauna ba karatu, su kuma da yaransu su ci gaba da mulki suna satar arzikin kasa. Sun kasa ganewa cewa illar rashin karatun yaran talakawan zai shafe su kamar yadda yanzun matsalar tsaro ya shafe kowa a kasan nan. Idan kana gadaran kana da masu gadinka ne, toh ya taba dan-uwanka kokuma zai iya taba dan-uwanka.

Zaka ga dan talakan da ya samu daman yin karatu idan ya gama saide ya zauna da takardarshi (Certificate) a gida, domin ba samu aiki zaiyi ba, sai daidaiku daga cikin yaran talakawan suke samun aiki idan suka gama. Shiko dan masu fada aji tun kafin ya gama karatu aiki nanan yana jiransa a babban ma’aikata. Saboda aiki a Nijeriya dole sai kasan wani mai fada aji kafin ka samu, shi kuma talaka, yasan talaka dan-uwanka shi ne. Idan kana dan talaka, kayi karatu ba aiki, ba kayi karatu ba ba aiki, sai mai ya rage, sai shigan miyagun ayyuka, sai wanda Allah ya tsare ne kawai zaiyi hakuri.

Ka duba harkan kiwon lafiya, wadansu garuruwan idan mutum bai da lafiya sai sunyi tafiya sama da kilomita dari daya (100 Kilometer) kafin su samu asibiti saboda rashin tausayin talaka a zuciyar masu mulki. Amma zaka ga mutum daya ya cire miliyon dari biyu (200m) ya saya mota daya, yana hawa, wanda kudin zai iya gina kananan asibiti a kalla guda koma sha.

Wadansu masu mulkin har jirgin sama suke dashi na biyan bukatunsu, amma kauyen da ya fito ana fama da rashin ruwa, ana fama da rashin titi da asibiti. Amma tunda ba talaka bane a gabanshi, zai hau jirgi kokuma motar alfarma, shi ba abinda ya dame shi.

Gasunan suna ta fade-fade akan dubu talatin karancin albashi (30 minimum wage) da ake ce za a karawa ma’aikata, wai su basu da kudin da zasu biya. Basu kudin da zasu biya dubu talatin a wata, amma akwai kudin da zaku sace ku saya motocin alfarma, ku gina gidajen alfarma, yaranku na shan sweets a wata na sama da dubu talatin. Amma baza ka iya biyan magidanci mai mata da yara dubu talatin a wata. A ciki zai ciyar da kanshi da iyalen shi, ya biya kudin makarantan yaranshi, idan yaronsa baida lafiya ya kai shi asibiti duka a dubu talatin. Amma kai mara imani, dan bakin ciki wai ba zaka iya biya ba.

Kuma zaka ce wani aiki suke yi jihohinsu, alhalin ba su aikin komai, an barsu kullum sai korafin ba kudi. Kuma duk karshen wata sai an tura musu da kudi daga gwamnatin tarayya. An basu (Bailout da basu Paris Club) duk sun cinye, sai kace wuta.

Kawai abinda masu mulki suka dauke mu talakawa mu dabbobi ne, bamu san abinda muke yi ba, sun dauke mu bayinsu ne da yaransu. Amfanin talakawa a gurinsu kawai idan siyasa ta juyo a zo a yaudare mu da dubu daya mu kada musu kuri’a su ci gaba da yi mana wulakanci.

Tsaka mai wuyar da talaka a Nijeriya ya ke ciki shi ne, kusan akasarin masu mulkin halinsu daya ne, rashin imaninsu daya ne, rashin tausayinsu daya ne, sai kunki zaban wannan kunce gara wancan, sai yaje tsiyar tashi tafi na baya.

Talakan Nijeriya gatanka Allah, talakan Nijeriya gatanka Allah, talakan Najeriya gatanka Allah. Allah shine wanda zai iya fidda talakan Nijeriya daga kuncin da yake ciki, domin kashi tasa’in da biyar (95%) na musu mulki a Najeriya basu da imanin talaka a zuciyarsu. Yana daya daga cikin abinda yasa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa cimma burinsa, saboda abokan aikin shi kansu suka sani da iyalensu. Saboda haka abu mawuyaci ne Muhammad Buhari yayi cimma burinsa sai an hada da addu’a. Allah ya taimake mu.

Allah ya shiryar mana da shuwagabanninmu, ya shiryar da mu kanmu. Duk wandanda bama su shiryuwa bane Allah ka fi mu saninsu, kayi mana maganin su.

Allah ya bamu zaman lafiya a kasarmu Nijeriya, ya bamu damina mai albarka. Amen.

Share.

game da Author