Dakarun Najeriya sun kashe Boko Haram hudu

0

A ci gaba da kakkabe burbudin Boko Haram da sojojin Najeriya ke yi a dajin Sambisa da wasu kauyukan Jihar Barno, dakarun Najeriya sun kashe wasu yan Boko Haram.

Kakakin rundunar Sojin Sagir Musa ne ya bayyana haka a sako da ya aiaka wa manema labarai.

Sagir yace tare da ahadin guiwar yan banga sojojin sun yi nasarar kakkabe burbudin Boko Haram a kauyukan Surdewalla, Ranwa, Baladayo, Sabon Gari Shetimeri, Mboa, Mboa-Kura, Yarchida, Bombula, Tshata da Bamzir.

Sagir ya ce a wannan aiki sun ragargaza Boko Haram da dama sannan sun kwato makamai a hannun su.

” Babu wani jami’i da ya rasu sai da wadanda suka samu raunuka na asibiti ana duba su.”

Share.

game da Author