DAWOWAR SARKI SANUSI: Kano ta dau zafi

0

A yau Asabar ne ake sauraron saukar jirgin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a filin jirgin Aminu kano bayan tafiya da yayi kasar Ingila.

Dubban magoya bayan sarki Sanusi da mutanen Kano ne suka yi tattaki zuwa filin jirgin saman domin jiran saukan jirgin sarki Sanusi.

Wasu da suka zanta da wakilin mu a Kano sun ce garin ya rincabe, masoyan sarki Sanusi sun fito kwansu da kwarkwata domin yi wa sarkin Lale-marhaban.

Ana sa ran jirgin Sarki zai sauka ne da misalin Karfe 4 na yamma a filin jirgi na Aminu Kano.

Har yanzu dai sarkin Kano Sanusi bai ce uffan ba game da daddatsa masarautar Kano da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje yayi.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya fasa masarautar Kano inda ya kirkiro sabbin masarautu har guda hudu.

Mutane da dama sun yi tir da wannan masarautu da Ganduje ya kirkiru suna masu cewa yana yi wa sarki bita da kulli ne kawai don siyasa ba wai don yaga hakan ya cancanta a yi ba ko kuma daukakar jihar Kano.

Cikin kwana uku kacal, majalisar jihar Kano karanta wannan kudiri da wani dan majalisa ya mika a gabanta. A rana ta karshe kuwa wato cikon na ukun, Kakakin Majalisa da wasu daga cikin wakilan majalisar suka garzaya fadar gwamnati inda nan take gwamna Ganduje bai yi wata-wata ba rattaba hannau a wannan kudiri ta zama doka.

Masarautun da gabduje ya kirkiro sun hada da Masarautar Karaye, Masarautar Rano, Masarautar Bichi da masarautar Gaya.

Share.

game da Author