Wasika zuwa ga Gwamnan Kano Dr Umar Abdullahi Ganduje, Daga Bilkisu Yusuf Ali

0

Zuwa ga Maigirma Gwamnan Jahar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Bayan Gaisuwa dafatan alheri dafatan an yi umara lafiya an dawo kan aiki cikin nasara Allah ya amshi ibada amin. Ya aka ji da hayaniya da fadi-tashin zabe?

Alhamdllah bukatar maje hajji sallah don haka muna addu’ar Allah ya rika maka amin. To amma fa Ur Excellency, bayan tiya akwai wata cacar don haka na rubuto maka wannan wasikar. Mu masu kishin jam’iyyar APC kuma masoya jam’iyya mu kadai muka san bacin rai da takaici da kunci da firgici da faduwar gaban da muka shiga a lokacin da aka kai iya wuya ranar zaben gwamna kafin tafiya Inconclusive.

Allah shi ne abin godiya a karshe jam’iyyarmu ta yi nasara kuma mun tsoma kafa a next level ko ba komai dodar ta tabbata.

To amma Bahaushe ya ce tuna baya fa shi ne roko! don haka zan hasko maka manyan kura-kuran da ka aikata na siyasa wanda shi ne muke gani Ummul aba’isin da ya kai mu ga tafiya Inconclusive.

Da a ce babu ko da rabinsu da ba mu girgiza ba har wankin hula ya kusa kai mu dare. Da tuni mun jijjige PDP tun da sanyin safiya kafin ma sha biyu mun lashe zabenmu kamar dai yadda muka yi a zaben shugaban kasa. Sannan an ce daga na gaba ake gane zurfin ruwa don haka duk mai hankoron maye gurbinka bayan shekaru hudu masu zuwa lallai ya tabbatar bai kuskura ya aikata irin wannan kuren a siyasa ba. Wadannan kuwa abubuwan sune:

1. Soke ilimi kyauta wanda aka faro a gwamnatin baya. Da a ce ka kamanta ko da a mataki guda ne ko Firamare ko kuma a Sakandare ne da ka kusanto kanka da iyayen yara wadanda duk ka ga xansa a wannan makarantun ka san talaka ne. Gaza hakan ne ya fara kulla maka gaba da talakawan jahar Kano. Dafatan a gaba za ka gwada yin haka sannan waxanda ba za a dau nauyinsu ba a ba su wani abu ko da ba yawa na abinci ko da sau daya ne.

2. Rabuwarku da Kwankwaso ta janyo ma ‘yar tsama tare da dakushe haskenka amma da ka bi halayyar da aka sanka da ita ta kau da kai da hakuri ka yi shuru da mayar da martani ga bangaren kwankwasiyya ka bar yaranka su tare maka fadan da ya fi maka.

Maimakon hakan ka ci gaba da yin ayyukan ka na alheri wanda shi ya janyo Kwankwaso na kan mulki amma Kanawa na cikin gwamnati da mu na gefe muka lashi takobin sai kai. Kuma Allah ya tabbatar da fatanmu. Amma sai ka gaza yin kwatankwacin abin da ka yi a bayan ka mulki zuciyar Kanawa.

3. Riikicin zaven ciyamomi na 2018 shi ma ya janyo fushin ‘yan jam’iyya. Na farko dai an tsula wa fama-faman Takarar ciyaman da kansiloli kudi kuma babu wani tallafi da jaha ta bayar. Sannan kowa ya san yadda aka yi zaben firamaren wanda daga fadarka a ka yi zaben na son zuciya. Ba za a ce laifinka ne 100% amma dai ka dau kaso mafi tsoka don kai ka sakar wa masu daidaikun ‘yan jam’iyya maimakon ka nemi ra’ayin talakawan da ke karamar hukumar.

4. Kananan ‘yan kasuwa musamman ‘yan tebura na kwari da na kasuwar kofar Wambai da sauran kasuwanni babu wani tallafi da ya zo hannunsu kai tsaye ko a kaikaice don harkar neman abincinsu wannan ya kuma sa wa adawa da gwamnatinka tana zagayawa .

5. Gaskiya a bangaren yada labarai ka sami matsala. Ba ka da masu yaki da baka ko a rubuce sam-sam. Wannan kuwa a bayyane yake ba wani tsari da aka fito da shi don yada ayyukanka da yada farfaganda ta siyasa a kafofin sadarwa. Misali makarantun da ‘yan adawa ke ta ya madidi Kwankwasiyya ta gina kuma ake zargin ka rufe ba wata hujja da tai ta zagayawa kan dalilan da yasa ka rufe su. Misali legal ta kunci wadanda ke da alaka da ilimi sun san yadda aka yi karo-karon malamai aka zuba su amma ba a yi wani tanadi ba na koyarwa. Da kansu malaman suka roki a mayar da su inda suka fito wanda sun san ba laifinka ne ba yaudararsu gwamnatin baya ta yi. watakil da ma an yada da hotunan kangwayen da watakila da Kanawa sun sasssauta daurin zanin da suka yi maka da tsanani a wannan bangaren. Amma ina! a kafofin facebook da tweeter da sauran kafofi inda anan ne ake wanke zuciyar matasa ake sa musu akida ake zayyana musu hujjoji na su so ko su ki to fa APC ba ta da wadannan sai ka kwana ka wuni ba ka ji wani abu na ci gab aba. Wannan ma fa kai kenan kada kwamishinoninka su ji labari su sun dauka har yanzu rayuwar Analog ce. Gaskiya jam’iyya na bukatar bita ta musamman a wannan gabar.

6. Karbar haraji a wannan gabar musamman ga kanann masu neman na abinci Gaskiya matsala ce musamman ma da ba fito da wata hanya don more rayuwar talakan ba. Sannan ma karbar harajin ba wani tsari da aka bi na hikima sai ku ka bar ‘yan adawa suka ci karensu ba babbaka. Musamman a harajin gidaje da na ‘yan adaidaita da na kuma ma’aikata. Shi fa dan Najeriya ma a batun harajin nan sai an yi masa bita.

7. matsalolin inshorar lafiya ga ma’aikata ita ma ta bar baya da kura maigirma gwamna. Rashin bayani da yin kudin goro da rashin tambayar jin ra’ayin ma’aikatan. Watakil da an bude abin ga mai so ba wai wajibi ba da ya fi zama dai-dai.

8. Zaben Fidda gwani da aka yin a ‘yan majalisun jaha da na tarayya Maigirma Gwamna shi ne ya janyo rabin matsalar da aka samu a zaven nan. Akwai wadanda suka cancanta talakawa ke sonsu amma sai aka bi sanayya da kara aka ki zabin talaka. Sannan zantuttuka sun yi ta zazzagaya wa cewar sai da aka bayar da na goro kafin a zabi mutum. Su wadanda suka bayar su suka din ga yadawa wannan ma ya sa da zabenka ya zo suka ce su ma kujerarsu saya suka yi don haka kowa tashi ta fisshe shi. Wadanda kuma suka cancanta ba a ba su takara ba duk kuwa da sun cancanta kuma suna da mutane suka ga gara su rama ta hanyar Anti fati ka san kome kuma nasan an sanar da kai ko su waye ba sai mun maimaita maka ba. In kuma kana bukatar ji mu muna da shaida.

9. Rikice –rikicen cikin gida da rashin kalamai mai dadi daga bakin shugaban jam’iyya ya sa ‘yan jam’iyya cire hannu da zuba ido sannan ya kara assasa rarrabuwar kai inda ake zaben ‘yan marina a jam’iyyar wato kowa da inda ya sa gaba.

10. Kafin zaben 2015 gwamna ya sa an yi kungiyoyi don yakin neman zabensa wadannan kungiyoyi sun yi aiki kuma ya sani amma da ya hau kan mulki ba wani tsari da ya bi wajen neman wadannan kungiyoyi a kyautata musu.

11. Rashin daukar ma’aikata kuma ko da za a dauka din sai mai kafa da dan siyasa. A bayyane yake aiki a jahar Kano sai ta hannun shugaban jam’iyya ko babban dan siyasa ko kuma yan majalisu na jaha ko tarayya amma talaka bai da ikon ya ji ana neman aiki ya nema ya samu. In ba ka sani ba Ya maigirma gwamna to ka sani talakawa kar suke kallonku a wannan bangaren . Za a yi shelar neman aiki amma tuni a karkashin kasa an rabe guraben. Wannan shi kara haska maka gaba da ‘yan boko ‘ya’yan talakawa don sun ga yadda a gwamnatin baya aka yi da wadda kai ma ka san yadda aka yin.

12. Rashin daukar nauyin karatun matasa masu digiri da daya da na biyu da na uku ya sa matasa sun ji kamar ba su ake mulka ba. Ka kuwa san da shi ku ka rudi Kanawa a shekarar 2011-2015. Me ya hana ka kamantawa? In kun kamanta me ya sa ba ku yayata ba? Yana da kyau daukar nauyin karatun wadanda suka fito da kyakkyawan sakamako a sakandire ko a makarantun gaba da sakandire musamman wadanda ba su da karfi kuma sai an tabbatar da ba su da hali. Ba fa sai an kais u kasashen waje ba a jami’oin kasar nan za a iya samo musu gurabe kuma za a sami kyakkyawan sakamako na jan ra’ayin talaka.

13 Maigirma gwamna a yi hakuri amma batun Gaskiya sanyin gwamnatinka da son ka kyautatawa kowa ya mayar da kai ba tsayayye ba a bangaren shugabanci. shi kuwa shugaba ana son a same shi tsayayye mai Magana daya kaifi guda marar tsoro. A fa mutane akwai ma fa wadanda su zuma ne sai da wuta. Za ka yarda da ni a haka in ka dubi kunshin kwamishinoninka da dama kai ka san ba mataimaka ba ne ka ma ga hujja a zaben nan wasu ma ka san ba ‘yan jam’iyya ba ne wasu kuma ba ‘yan siyasa ba ne, wasu ramin kura ne daga su sai ‘ya’yansu wasu kuwa irin wadanda iyayensu ba sa mutuwa ne a siyasa tun daga lokacin malam Shekarau suke rara gefe da kai zance amma abin mamaki sai ga su a hannun damanka sun shallake kowa. Kuma suna nan jikinka amma suka tafi taya PDP yakin neman zave kowa ya gansu. Ba a yi mamaki ba don da ma an san duk wanda ya sai rariya yasan za ta zub da ruwa. Ka yi tsam in ma da hali ka sa a yi ma kyakkyawan nazari a kunshin kwamishinoninka tunda suka hau zuwa zave sau nawa kowanne aka ja sunan sa a radiyo ko talabijin ko ma a kafofin sadarwa ta zamani? In da zan rantse bazan yi kaffara ba za ka sami wani ba a ja sunansa sau uku ba. Amma za a ce ba a ji sunan wasu ba?

14. Tsarin da ka assasa na ‘ya’yan bora da mowa a gwamnatinka ya janyo rarrabuwar kai da rashin taimakon gwamnatin ta kowanne janibi. Maigirma Gwamna ana zarginka da fifita wasu da kuma danne wasu a cikin gwamnatin. Wasu an sakar musu dama suna damawa wasu kuwa an kyale su talakawa da abokanan adawa suna tunzura su. Adalci a matsayinka na gwamna na da muhimmanci.

15. Yaudara da rashin cika alkawari na damun talaka. Misali a kwanan baya aka sa yara masu N.C.E suka yi tururuwa suka fito ‘ya’yan talaka za a dauke su koyarwa amma ashe ba haka ba ne hatta a baya an ce al’umma su fito su bude asusun ajiya a bankin sitalin kai ne za ka tsaya a ba su kudin jarin. Mu ka yi ta yayatawa amma daga baya a bankin in ka je ka tambaya ya shuru sai su ce ai zancen ‘yan siyasa ne kawai. Ire-iren wannan da dama wanda da ya kamata in har an san abu ba zai yi wu ba to kada a fara ya fi alheri. Ko kuma a yi dai-dai ruwa dai-dai tsaki.

16 . Kananan hukumomi fa mai girma gwamna sun zama tamkar zaman kare a karofi. Ba wani abu da yake zagaya wa Kuma nan talaka yake. Anan ne a ke zabe a nan ne matansu da ‘ya’yansu mata ke fitowa kome zafi kome sanyi su dangwala kuri’a amma sun fi kowa shan wuya da zama abin tausayi. Da za a samar da wata santa a duk karamar hukuma ta din-din-din don tallafawa yan karamar hukumar ta koya musu sana’a da ta yaki da jahilci ta ka assasa wani alheri da za a gani.

17. Rashin bibiya bayan ka danka amana ta aiki a hannun wasu sannan a hukunta duk wanda aka samu da cin amana a fili tare da fito da hujjojin da aka kama mai laifin a bayyane. Zai taimaka kwarai wajen ayyukan da aka yi don talaka ya isa gare shi.

18. Akwai waxanda suka shigo jam’iyyarmu ta APC daga PDP kuma sun taka muhimmiyar rawa a tafiyar ya kamata in aka zo raban mukamai kada a manta da su don kuwa da su za a tsara tafiyar 2023. Don kuwa sun taka rawar da dama ‘yan jam’iyya ba su yi kwatanta ba, sannan ragowar ‘yan’uwansu da ke PDP da PRP kun dai ga tasirinsu a can wannan dama ce da za a janyo su don sharewa dan takarar Gwamna hanya a 2023 in Allah ya nuna mana.

19. Batun Gaskiya maigirma Gwamna ka tula dattijai a gwamnatinka babu matasa kuma matasa a kowacce nahiya sune ruhin al’umma su ne suke da kishi da karfin gwiwa da karsashi da rashin nauyi da kurde-kurde kuma su ke shiga cikin al’umma su sake saboda rashin nauyin da ke kansu don haka su ne suka fi jin me al’umma musamman ‘yan’uwansu matasa ke ciki. Kai hatta a wajen yada ayyukan gwamnati da farfaganda da sanin hanyoyin sarrafa na’uororin zamanin nan sune a kan gaba ya kamata a ba su dama. In ka lura jam’iyyar adawa abin da ya sa ta wannan farin jinin ai matasa ne.

20. Maigirma gwamna ko ka sani ko ba a sani ba iyalanka musamman mai kakinka ta shiga cikin gwamnatinka ta yi kaka-gida har jama’a sun gane in ana son wani abu a gwamnatinka fa sai an yi kamun kafa ta hanyar kai gaisuwa da bayar da na goro. Wannan nakasu ne a gwamnatinka da ‘yan adawa ke sukar ka da shi kuma ka sani sukar na yin tasiri. Hotunan da ke yawo a social media da ire-iren hotunan ya ishi shaida. Sannan bayanan sirri da hotunan iyalanka mata kan fito da shiga wadda a matsayinka na Bafulatani mai riko da addini bai kamata ba. Kada ka manta har yanzu kano suna nan fa da rikon al’adunsu da aka san su da shi da kuma kamanta addini.

21. Akwai ‘yan Lagasi fati wadanda aka hadu aka yi APC maigirma gwamna su ma fa korafinsu a bin dubawa ne. Misali a gwamnatin baya da ku ka faro da maigirma Kwankwaso ya zamana duk mataimakin shugaban karamar hukuma dan lagasi ne sannan an saka su a gwamnatin amma a lokacinka sai ya zamana an mayar da su aljihun baya. Wannan ya sa suka nade hannayensu suka zuba ido su ma.

22. Maigirma gwamna akwai rashin tallafi ga ma’ikatanka kama daga kwamishinoni Ciyamomi har kansiloli an bar su babu wani welfare kwamishina na kukan babu yana jiran a yi albashi ciyamomi da an bayar da giran yau gobe babu ko dubu bare kansiloli ba me kallonsu da kima. Wannan kuskure ne kudin nan fa na karamar hukuma shi ne ke tallafar na kasa wato talaka da su ake kananan ayyuka kamar kwalbati gyaran makarantun firamare gidan wani ya rushe ibtila’i ya fada ma wasu ko gyaran makabarta ko kasuwa da sauransu. Bai kamata ka matse mataimakanka ba kamar yadda muke ji na kusa da su na fadi da abin da su suke fada da abin da idonmu ya gane mana in har a next level aka ci gaba da haka to fa ba a yi wa mai jiran gado kyakkyawar shimfida ba. Ya kamata a girmama su kamar yadda gwamnatocin baya ke yi.

23. Matsalolin ‘yan kwangila Maigirma gwamna a kuma dubawa. Akwai son zuciya da rashin tabbas da ma zubewar kimar kwangilar a Kano. Misali ‘yan kwangila na kukan bayan sun bayar da 25% ko 30% na al’ada sai kuma a bijiro musu da wasu wadanda ba su da ma hurumi a kwangilar a ce su ma a ba su wani kaso. Babbar illar da za ta biyo shi ne Samar da ayyuka marassa inganci.

A karshe maigirma gwamna ina kara taya ka murna da yi ma fatan alheri. Kamar yadda aka saba ayyukan alheri kowa ya sanka da zumunci da son addini da kunya da girmama manyanmu muna fatan ka dore.Ina rokon a kalli wasikata da idon basira kafin ka nada sababbin kwamishinoni da mukarraban gwamnatinka don kada ka kuma yin kitso da kwarkwata duk wanda bai taka rawa a zaben da ya wuce ba ko ma ya yi Anti-fati muna fatan za ka ajiye shi don ba shi da amfani.

Bissalam
Sai ka kuma ji na in har na ga kunshin kwamishinoninka. Zan bi su daya bayan daya in yi warwara kansu in har irin wadancan taron tsintsiyar ne ba shara.

Bilkisu Yusuf Ali (Dr)
bilkisuyusuf64@gmail.com
08064159965

Share.

game da Author