Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar cewa ba za yi wasu shagulgula ba a lokacin sake rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya bayyana haka jiya Litinin a Abuja, a lokacin da ya ke hira da manema labarai.
Lai ya ce za a jinkirta wasu abubuwan da za a yi a lokacin rantsarwar, har sai ranar 12 Yuni tukunna, wadda ita ce sabuwar Ranar Dimokradiyya a Najeriya.
Ya ce taron da Majalisar Zartaswa ta gudanar na ranar Laraba, 8 Ga Mayu ne ya zartas da cewa kada a yi shagulgula a ranar sake rantsarwar.
Amma kuma Lai ya yi karin hasken cewa an tuwa wa dukkan shugabannin kasashen duniya takardar gayyatar bikin Ranar Dimokradiyya a ranar 12 Ga Yuni.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta iya daukar nauyin gudanar da shagulgula biyu a cikin mako daya ba. Sannan kuma za a yi taron ‘yan jaridu na duniya a ranar 20 Ga Mayu, a Abuja.
Buhari ya lashe zabe karo na biyu, bayan kayar da dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar. Sai dai kuma za a yi wannan rantsarwar ce a lokacin da tuni Atiku ya maka APC, Buhari d kuma INEC a kotu, inda ya ke kalubalantar nasarar.
Atiku ya yi ikirirarin cewa shi ne ya yi nasara, aka yi masa magudi.