Mahara sun kashe ‘yan sintirin CJTF shida a wani hari a cikin Karamar Hukumar Shinkafi. Haka Mataimakin Karamar Hukumar, Sani Galadima ya bayyana.
Galadima ya bayyana haka jiya Litinin a lokacin da ya karbi bakuncin Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurrahman Damnazau.
Dambazzau ya je Zamfara ne saboda wani sabon yunkuri da gwamnatin tarayya ke yi domin ganin an magance matsalar rashin tsaro da ake ta fama da ita a jihar.
“An kashe CJTF shida jiya Lahadi, bayan an biya su kudaden alawus din su a cikin garin Shinkafi. An yi musu kwanton-bauna an kashe su a kan hanyar su ta komawa kauyukan su.”
“Ko jiya ma sai da wadannan mahara suka aiko wasika zuwa ga Dagacin Shinkafi cewa za su shigo su kawo wa Shinkafi hari.
” Wannan mumunan halin kuncin da mu ke cikin abin damuwa ne matuka.Mu na bukatar taimakon gaggawa daga bangaren gwamnati, domin kawo karshen wannan bala’i.
“Matan mu na shiga halin kunci sosai, saboda mahara na shiga kauyuka su na kwacen ‘yan mata su gudu da su. Yanzu a Shinkafi mutane ba su iya barci sosai saboda tsananin fargabar lokacin da ‘yan bindiga za su kawo hari.
” Mu na so gwamnati ta magance matsalar karancin sosoji da ‘yan sanda da ake fama da ita a kasar nan. Saboda gaba daya a Shinkafi sojoji 19 ne mu ke da su masu kula da garin.
“Mu na bukatar karin dauki daga gwamnati, saboda mu dai a gaskiya ba mu gamsu da kokari da kuma irin takun da jami’an tsaro ke yi a kan matsalar tsaro ba.
” Duk fa mun san inda sansanin maharan nan suke. Su ma sojoji duk sun san inda suke. Amma babban abin da ke damun mu shi ne yadda su jami’an tsaro ba su iya zuwa inda ‘yan bindigar su ke.” Inji Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi.
Galadima ya ce akalla mazauna kauyuka 98 duk sun gudu daga yankunan su saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Da ya ke jawabi, Dambazau ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya tura shi Kananan Hukumomin Shinkafi da Anka domin gano hanyoyin magance matsalar.
Ya kuma ce ya rigaya ya je Anka, kuma a kokarin da ake yi, sun yi taro da Kungiyar Miyetti Allah.
Discussion about this post