Boko Haram sun kashe kwamanda da sojoji biyu

0

Akalla sojoji uku ne suka rasa rayukan su, wasu gudu suka ji raunuka yayin da bam ya tarwatsa wani jerin gwanon motocin sojoji a jiya Litinin.

Cikin wadanda suka mutu har da Laftanar Kanar da kuma direban motar, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.

PREMIUM TIMES ta sakaya sunan Laftanar Kanar din, saboda har hukumar sojoji ba ta kai ga bayyana wa iyalan sa halin da ake ciki ba tukunna.

Sojojin jerin gwanon da abin ya shafa na Bataliya ta 145 ne, wadanda ke kan hanyar sintiri. An dasa bam din da ya tashi da su ne a gefen titi, kuma ya yi musu barna a daidai 9:30 na safiya. An kai musu hari ne a kan hanyar Mauli zuwa Borgozo, daya cikin sauran ‘yan yankunan da Boko Haram ke kai wa hari.

Amma nan da nan an tura musu karin sojoji daga Brigade na 29 da ke Benisheikh da Bataliya ta 154, wadanda suka kwaso gawarwaki da wadanda suka ji ciwo.

Majiya ta ce motar yaki guda biyu wadanda ake yi wa zabarin babbar bindiga sun lalace. Akwai wata motar sojoji samfurin Tata, ita ma ta lalace.

Kakakin sojoji bai dauki waya ba, ballantana a ji ta bakin sa. Sannan kuma har zuwa 7 na safiyar Litinin na su fitar da wata sanarwa a kan lamarin ba.

Share.

game da Author