ZARGIN MADIGO: Yadda Hadiza Gabon ta ci zarafin Amina Amal, ta rika sharara mata mari da tsangwama

0

A wani Bidiyo da ya rika yawo a shafunanan jaruman Kannywood, ya nanu yadda jaruma Hadiza Gabon ta rika sharba wa Jaruma Amina Amal mari a killace a daki tana mata tambayoyi kan wani sakon Tes da ta aika mata.

A wannan Bidiyo, an rika jin Gabon tana cewa a bata wuri ta lakadawa Amal dukan tsiya cewa ta yi mata kazafi.

Sai dai kuma, da yaki abin har da fin karfi, Amal ta yi zukgum zaune a kan gado tana sauraron Gabon, inda ta rika cewa sai ta karanta wasikar da ta rubuta mata ta waya.

Wani dake tare da Gabon din a wurin yayi kokari hana ta ci gaba da dukan Amal da ta ke yi amma hakan bai yiwu inda daga baya shine ya karanta sakon.

Kamar yadda ya karanta sakon Abin da ya kusa cewa tayi, ” Salam, Yar uwata, don Allah idan bakya komai anjima, ina son ganin ki, Ma’assalam.”

Ma su karatu da dama da wasu abokanan aikin su, sun kushe wannan abu da Gabon ta yi inda wasu suka rika cewa hakan ta’addan ci ne da nuna fin karfi.

” Ni banga wani abin da ya nuna wai Amal ta nemi Gabon don wani kusanta bane da ya wuce na kawance kamar yadda ta bayyana a wasikar.
Ya kamata irin haka manya su saka baki a akai sannan su bi wa wannan baiwar Allah hakkinta.” Inji masu Karatu da dama.

An dade ana zargin ‘yan Kannywood din da Madigo a tsakanin su inda a shekarar 2016, jarumai irin su Adam zango da Mustapha Naburaska suka fito karara domin kushe abin na bayyana cewa basu cikin irin masu yin wannan harkar. Sun rantse har da Alkur’ani.

Share.

game da Author