Tawagar gwamna El-Rufai ya fada wa masu garkuwa a hanyar Kaduna zuwa Abuja

0

A daidai misalin karfe 3:40 na yammacin Laraba ne gwamna Nasir El-Rufai ya fada wa masu garkuwa a daidai suna kokarin yin garkuwa da mutane a titin Kaduna zuwa Abuja.

Mahara sun tare titin Kaduna zuwa Abuja da yamman Laraba a daidai gwamnan jihar Nasir El-Rufai zai tafi garin Abuja.

Ko da ya iso wani gari da ake kira Akilibu, sai ya ci karo da dandazon motoci suna tsaitasaye wai mahara ne suka fito suna sace mutane.

Sannan kuma ga wasu nan wadanda aka harba a kwankwance.

El-Rufai ya umarci masu tsaron sa da su bi su hanyar su fatattaki maharan. Daga nan sai suka arce cikin daji da makaman su.

Bayan haka ne mutane suka ci gaba da wucewa zuwa inda za su tafi.

Share.

game da Author