Babbar Kotu a Abuja ta soke takarar Ademola Adeleke na PDP, a zaben gwamnan Jihar Osun da aka gudanar cikin Satumba, 2018.
Mai Shari’a Othman Musa ne ya yanke wannan hukunci bayan da ya ce Adeleke ya kasa gamsar da kotun cewa ya kammala makarantar sakandare, kamar yadda ka’idar shiga takarar gwamna ta gindaya a cikin Sashe na 177 na Kundin Dokokin Najeriya.
Adeleke dai ya yi takarar gwamna, amma Adegboga Oyetola na APC ya kayar da shi a wani zabe da aka gunadar a cikin Satumba.
Amma Adeleke ya kai kara cewa shi ne ya yi nasara ba dan takarar APC ba.
A ranar 22 Ga Maris, Babbar Kotun Tarayya ta bai wa Adeleke nasara, tare da cewa zaben da aka maimaita a wata rumfa ranar 27 Ga Satumba, wanda shi ne ya bai wa dan takarar APC nasara, haramtacce ne, bai kamata a maimaita shi ba.
Sannan kotu ta umarci INEC ta bai wa Adeleke satifiket na shaidar yin nasara a zaben.
Sai dai kuma dan takarar APC ya garzaya kogtu tare da kalubalantar wannan hukunci da kotu ta soke nasarar da ya yi.
To kuma ana wata ga wata. Wannan hukunci na baya-bayan nan da Babbar Kotun Tarayya ta yanke inda ta ce takardun Adeleke na kammala sakandare jabu ne.
Adeleke ya shaida wa kotu cewa ya kammala Muslim High School, Ede ta Jihar Osun, domin babu sunan sa a cikin jerin daliban da suka kammala makarantar a cikin 1980.
Duk da cewa ya hada wasu shaidu da suka kammala makarantar a lokaci daya, kotu ta ce an gan cewa sunan sa ya fiito ne a cikin sunayen wadanda suka rubuta jarabawar Turanci kawai.
Adeleke ya ce shi ma zai daukaka kara.
Discussion about this post