Hukumar Zabe ta mika wa Ganduje shaidar sake zaben sa gwamnan Kano

0

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta mika wa zababben gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC Satifiket din yin nasara a zaben gwamnan jihar.

An yi bukin bada satifiket din ne a zauren Sani Abacha dake gidan gwamnatin jihar.

A jawabin sa bayan ya karbi shaidar, Ganduje ya bayyana cewa zai ci gaba da ayyukan raya kasa a jihar Kano kamar yadda ya somo a karon farko.

” Za mu bude kofofin saka jaria a jihar Kano. Duk wanda yake da burin kafa masana’anta ya zo garin Kano zamu bashi duk gudunmawar da yake bukata domin haka.”

Baya ga Ganduje, an mika wa mataimakin sa Gawuna da ‘yan majalisun jihar.

Sai dai kuma duka ‘yan majalisan jihar na jam’iyyar PDP ba su halarci wannan taro ba.

Jam’iyyar PDP a jihar Kano bata amince da sakamakon zaben da ya bayyana Ganduje a matsayin wanda yayi nasara a zaben ba.

Tuni har jam’iyyar ta shigar da karara kalubalantar sakamakon zaben.

Share.

game da Author