Kungiyar Rotary International ta bada gudunmawar dala miliyan 5.7 domin kawar da cutar shan-inna a Najeriya

0

Kungiyar ‘Rotary International’ ta tallafa wa gwamnatin dala miliyan 5.7 domin kawar da cutar shan inna a kasan.

Kungiyar ta danka wadannan kudade ne ga wakiliyar UNICEF dake kasar nan Pernille Ironside a makon da ya gabata a Abuja.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya jinjina wa wannan kungiya bisa tallafin sanna ya ce Najeriya zata ta maida hankali wajen ganin ta kawar da cutar kwata-kwata a kasar nan.

Adewole ya kuma yaba kokarin da hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) game da ayyukan kawar da asha-Inna.

Share.

game da Author