Hukumar kwastam ta sanar da dibar sabbin ma’aikata 3,200 a fadin kasar nan.
Kwastan ta sanar da haka ne a sanarwa da ta fitar. Bayan haka ta sanar da shafin da za a iya neman aikin ta yanar gizo.
A sanarwar, hukumar ta ce za a rufa amsar bayanan masu neman aiki ne ranar 7 ga watan Mayu sannan kuma ta ce ba za a amshi takardun duk wanda ya mika takardunsa a ofisoshin hukuma ba ko hedikwatarta dake Abuja.
” A shafin hukumar na yanar gizo ne za a bi don cika fom din neman aikin kwastan din.
Ga shafin da za a bi – www.vacancy.customs.gov.ng
Discussion about this post