Tambuwal ya kama hanyar maimaitawa

0

Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ne ke kan gaba a kananan hukumomi biyar daga cikin shida na jihar Soko da aka bayyana sakamakon su ya zuwa yau lahadi da rana.

Daga cikin kananan hukumomi shida, Tambuwal na PDP ke kan gaba a kananan hukumomi biyar, yayin da APC ke gaba a karamar hukuma daya.

Tambuwal ya na takarar sake zama a kan kujerar ce a karkashin PDP, yayin da babban abokin takarar san a APC, Ahmed Aliyu ya samu nasara a karamar hukumar daya tal kadai.

Yayin da Tambuwal, wanda tsohon kakakin majalisar tarayya ne, wanda ya fice daga APC ya koma PDP a lokacin da ya ke gwamna, shin kuma Aliyu ya na takara ne a bisa goyon bayan Sanata Aliyu Wammako, wanda shi kuma ya yi gwamnan jihar Sokoto zango biyu, kuma ya na kan kujerar sanata a karo na biyu a yanzu.

Wamakko ya sake lashe kujerar sa ta sanatan Sokoto ta Arewa a karkashin APC.

Sakamakon kananan hukumomin da aka bayyana a Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe ta Sultan Maccido, Tambuwal ya samu kananan hukumomin Bodinga, Silame, Binji, Kware da Tureta.

Shi kuma Aliyu ya samu Karamar Hukumar Rabah.

Sokoto na da kananan hukumomi 23.

A Rabah APC ta samu 16, 535, PDP 13,232.

A Kware PDP 20,111, APC kuma 19,001.

A Binji PDP 12,367, ita kuma APC 10, 699.

Share.

game da Author