ZABEN GWAMNA: Yadda talakawa suka rika saida ’yancin su -CCD

0

Cibiyar Inganta Dimokradiyya (CCD) ta ce zaben da aka gunanar na gwamnoni da majalisar dokoki a jiya Asabar, an samu yawaitar wurare da dama inda masu zabe suka rika tsere sayar da kuri’un su ga duk wani ejan na dan takarar da ya fi biyan farashi mai tsada.

Shugaban Sashen Bin Diddigi na CCD, Adele Jinadu ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

Ya ce duk da ganin idon jami’an INEC da jami’an tsaro, ciki har da na EFCC, hakan bai hana dimbin jama’a sayar da kuri’un su ba.

Jinadu ya ce cibiyar su ta tura masu sa-ido a jihohi da dama, kuma ta tabbatar da haka.

CCD ta kafa misali da yadda EFCC ta kama masu sayen kuri’u a Benuwai da Kwara.

Rahoton ya ci gaba da nuna cewa a fii aka rika yin cinikin kuri’u ga wanda ya fi baiya da tsada, to shi ake sayarwa.

Akwai misali kuma a Rumfar Zaben Madobi PU 011 a cikin jihar Kano, an rika sayar da kuri’a daya daga naira 3,000 zuwa naira 4,000.

A wasu rumfunan zabe a Lagos kuma, CCD ta ce an rika saye naira 1,500.

A unguwar Isoko-Kosofe a Lagos, wani dan siyasa ya rika cunna wa jami’an zabe naira 5,000, amma suka ce ba za su karba ba, sai dai idan zai ba kowanen su naira 40,000.

Ya ce kuma magoya bayan manyan jam’iyyu sun rika yin basaje su na fitowa a matsayin ejan na kananan jam’iyyu sun a sayen kuri’u daga hannun mabukata.

Share.

game da Author