Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta soke hukuncin wucin-gadi da ta bayar, inda ta bayar da umarnin dakatar da tattara sakamakon zabe da kuma bayyana wanda ya ci takarar gwamna a Jihar Bauchi.
Cikin makon jiya ne kotun ta saurari kukan dan takarar gwamnan Jihar Bauchi na APC, wato gwamna mai ci yanzu, inda ta ce kada a ci gaba da tattara sakamakon.
Lauyan Abubakar, Ahmed Raji, ya garzaya kotu inda ya nemi ta hana INEC ci gaba da tattara sakamakon zabe.
Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya ce babu wani lokaci da kotun sa ta taba amincewa da wani kuka da Babban Lauya Ahmed Raji ya kai a gaban ta.
Ya ce wancan hukuncin da ya bayar, ai na wucin-gadi ne, kuma ba mai dadewa har tsawon wasu kwanaki masu yawa ba ne.
Daga nan sai ya ce a yanzu Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC za ta iya ci gaba da tattarawa da kuma bayyana sakamakon zaben.
Dama kuma INEC ta bayyana cewa za ta ci gaba da tattara sakamakon Karamr Hukumar Tafawa Balewa wand aba a kammala tattarawa ba.
Dan takarar jam’iyyar PDP, Bala Mohammed ya yin nasara a zaben da aka gudanar a ranar 9 Maris, 2019. Kuma shi ne yay i nasara a zaben da aka maimaita a ranar 23 Ga Maris, 2019.