Kotun daukaka kara ta soke ‘yan takaran APC na jihar Zamfara tun daga kan gwamna

0

Idan ba a manta ba Kotun Daukaka Kara dake jihar Sokoto ta amince wa jam’iyyar APC da duka ‘yan takarar ta su fafata a zabukan da aka gudanar a makonnin da suka gabata.

Wannan zabuka kuwa sun hada da zaben gwamna da sauran su.

Bayan haka ta Umarci hukumar zabe da ta amince da duka ‘yan takaran da jam’iyyar ta mika mata.

Wannan hukunci da Kotun ta yanke ya ba jam’iyyar daman fafatawa a zabukan Majalisun Kasa da na jiha sannan kuma da na gwamnan jihar.

Alkalai uku da suka saurari karar sun ce sun yi watsi da daukaka karar da aka yi ne bayan wanda ya shigar da daukaka karar Aminu Jaji ya janye karar.

Sanata Kabiru Marafa ne ya sake garzaya kotun daukaka kara, domin a bi ba’asin wanna hukunci da da aka yanke sannan a duba ainihin korafin da ake yi game da zaben da a ka gudanar.

A hukuncin da kotun ta yanke, tace babban kotun shari’a da ta ba APC damar mika ‘yan takara ba ta yi dai-dai ba.

Kotun ta ce a bisa bayanan da ke gabanta, babu wani dan takara da APC a jihar Zamfara ta iya tsayar wa har zuwa lokacin da aka rufe karbar sunayen ‘yan takara.

Alkalan kotun sun bayyana cewa irin wannan hukunci zai zama wa mutane da jam’iyyu darasi karara, cewa doka ba abin da za ayi wasa da shi bane.

Idan har ba wani abun da bam bane kotun koli ta yanke, shike nan dole APC da ‘yan takaran ta su tattara nasu-ina-su su dawo gida.

Share.

game da Author