Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ya ce batun wani abu wai shi zaben da bai kammalu ba, abu ne bambarakwai, wanda dokar Najeriya ba ta ma san da shi ba.
David Mark ya yi wannan jawabin ne a gidan sa da ke garin Oturkpo, Jihar Benuwai, ranar Asabar da ta gabata.
Ya bada shawara ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC da ta guji bayyana cewa zabe bai kammalu ba.
Ya ce ta haka INEC ta za rage yawan makudan kudaden da ake sake kashewa wajen sake zabuka a mazabun da aka ce zaben bai kammalu ba.
Mark ya ce zabukan da ake same maimaitawa su na zuwa da sarewa, jigata da gajiya ga ‘yan siyasa da su kan su masu zabe.
Daga nan sai ya ce ya kamata INEC ta rika yin karfin hali ta na yin abin da ya dace.
Mark ya nanata cewa maganar wani zabe wai shi wanda bai kammala ba, bakon abu ne ga dokar Najeriya, domin ba ta ma san da shi ba.
“Idan batun zaben da bai kammalu ya samu gindin zama a cikin siyasar mu, to zai iya bada dama ‘yan siyasa su rika hargitsa zabuka ko sakamakon zabe, yadda idan za a maimaita, sai su sake yin gagarimin shirin yin magudi, ko kuma cin zaben da tsiya ko da tsinin tsiya.’’ Inji Mark.
MA’ANA TA FARKO: INEC na cewa zabe bai kammalu ba idan ratar kuri’un da wanda ya yi nasara ko wanda ke kan gaba da kuma wanda ya yi na biyu, ba su kai yawan kuri’un da aka soke ba. Don haka dama a rubuce ya ke a dokar INEC cewa idan hakan ta faru, to za a sake zabe a wasu rumfunan da aka yi tankiyar kuri’un da aka soke.
ME DOKAR ZABE TA INEC TA CE?
Dokar Zabe ta Sashe na 153 ta jaddada cewa matukar ratar yawan kuri’un wanda ya zo na daya shi da wanda ya zo na biyu ba ta kai yawan kuri’un da aka soke ba, to zabe bai kammalu ba, har sai an sake yin zaben raba-gardama a yankunan da aka soke kuri’un.
INA MATAKAN RASHIN KAMMALUWAR ZABE?
Cikin wata doguwar makala da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya taba gabatarwa, bayan hawan sa shugabancin INEC, ya ce:
INDA HARGITSI YA HANA A YI ZABE
“A zabukan da suka gabata can baya, ’yan siyasa kan hargitsa zabe a inda suke ganin ba su da karfin samun kuri’u, ta haka sai su yi nasara a yankin da suka fi karfi. A kan haka ne a yanzu sai INEC ta ce idan aka hargitsa zabe a ko’ina, to INEC za ta sake bai wa jama’ar wannan yanki damar sake jefa kuri’a. Saboda kuri’a ce a kasar nan ke zabar mutum, don haka tilas ita ce za ta yi aiki kenan.
INDA ZABE BAI KAMMALU BA TUN A MAZABU
“Sannan kuma akwai inda ake samun zabe bai kammalu ba tun ma a mazabu. Gaba dayan dalilin bayyana hakan shi ne domin a bai wa jama’a damar jefa kuri’ar su. Domin kuri’a ce abin amfani ko dogaro a wajen zaben shugabannni. To idan an fahimci abin da duk na bayyana, sai kuma mu dawo, shin me ya sa ake samun zabukan da ba su kammalu ba?
DALILAN SAMUN RASHIN KAMMALUWAR ZABE
“Na farko dai akwai sabon sauyin canji a zabukan 2015, musamman sakamakon shigo da na’urorin zamani wajen zabe. Amma dai duk da hakan, ba mu kai ga matakin da ake son a cimma ba. A karon farko a zaben 2015 an samu karancin ratar kuri’u tsakanin jam’iyyar da ta yi nasara da kuma wadda aka kayar. Kuri’a milyan 2.5 ce mafi karancin yawan ratar kuri’u a zabukan shugaban kasa tun daga 1999.
“Na biyu kuma a da an saba ganin jam’iyyar da ta yi nasara na tserewa fintinkau da rata mai yawa sakamakon karfinta da kuma karancin karfin tarkacen kananan jam’iyyun adawa. Amma a yanzu kuwa akwai manyan jam’iyyu biyu masu karfi.
“Na uku kuma, akan samu takara ta yi zafi sosai. Kun ga an samu gaggan ‘yan takara biyu da suka fito daga manyan jam’iyyu biyu kenan. Kun ga kenan akan samu inda manyan jam’iyyu biyu sun fito da gaggan ‘yan takara biyu.
Wani dalilin kuma shi ne, yadda a yanzu zabe na kara samun inganci, inda a yanzu kuri’a ce ke tabbatar da sakamakon zabe. Duk inda ka duba sakamakon kowane bangare, za ka ga cewa ratar ba ta da yawa sosai. Wannan kuwa na nuna maka yadda takarar ke kara zafi sosai kenan.