A ranar Talata ne babbar kotun dake Apo a birinin tarayya Abuja ta gurfanar da sanata Dino Melaye a dalilin kokarin kashe kansa da ya nemy da wasu laifuka guda shida.
Lauyan da ya shigar da karar Alex Izinyon ya bayyana cewa Melaye ya aikata wadannan laifuka ne a ranar 24 ga watan Afrilu 2018.
Ya ce Melaye ya yi kokarin tserewa daga hannun jami’an tsaro a lokacin da jami’an tsaron ke kokarin kai sa ofishinsu dake Lokoja inda Melaye ya dirko daga cikin mota a daidai ya na tafiya.
” Ya kuma rike wani makami a hannunsa inda yake yi wa jami’an taron barazanar kashe kansa domin saka su cikin mummunar matsalar sannan ya fasa gilashin motar ‘yan sandan da hannunsa.
Melaye wanda ya lashe zaben kujerar sanata na mazabar Kogi ta Yamma a zaben da aka kammala ranar 23 ga watan Fabrairu ya ki amincewa da aikata wadannan laifuka.
Oriji ya bada belin Melaye akan Naira miliyan biyar tare da gabatar da shaidu biyu dake rike da babbar matsayi a aikin gwamnati kuma mazauna garin Abuja.
Sai dai kuma anyi hakan ne ba tare da an samu wakilcin lauyan Melaye, Mike Ozekhome a kotun ba.