Kungiyar kwadago reshen jihar Filato (NLC) ta yi kira ga dukka ma’aikata da su tabbata sun zabi ‘yan takarar da za su share musu hawaye ne a zaben da za ayi ranar 9 ga watan Maris.
Gunshin Yarlings ya yi wannan kira ne ranar Litini a garin Jos bayan kwamitin zantaswa na kungiyar ta kammala zama.
Yarlings ya ce ya yi wannan kira ne domin kara nanata kiran yin haka da shugaban hukumar na kasa Ayuba Wabba ya yi wa ma’aikata kafin a fara zabe.
Ya yi kira ga mutane da su nisanta kansu da duk wani abin da ka iya tada rikici a lokacin zabe.
” Duk da cewa kowa na da ra’ayin zaban duk dan takaran da yake so amma zabo ‘yan takarar da suke da ra’ayin ma’aikata zai fi mana amfani domin a shirye muke mu zabi duk dan takarar da ya amince ya biya ma’aikata da tsarin biyan albashi na Naira 30,000’’.
Bayan haka Yarlings ya jinjina janye karar kin biyan ma’aikatan da suka yi yajin aiki albashinsu a kotu da gwamna Jang ya shigar, biyan bashin albashin ma’aikata na tsawon watanni hudu bayan ta amince ta yi amfani da dokar ba aiki ba albashi,biyan bashin albashin ma’aikata da fansho na tsawon watanni bakwai da gwamnan jihar Simon Lalong ya yi.
Ya kuma yi kira ga gwamnanti da ta yi kokarin biyan ma’aikata da aka zaftare wa albashi a dalilin kin amfani da tsarin biyan albashi na Naira 18,000 duk da cewa tsarin ya yi shekaru biyar da gwamnati ta amince da shi.
Discussion about this post