Duk dan jagaliyar da ya hargitsa zabe a Kwara, sai dai uwar sa ta haifi wani – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ya ce jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben Gwamna da na Majalisar Dokokin Jihar Kwara da rata mai yawa a ranar Asabar mai zuwa.

Minista Lai, wanda shi ne jagoran APC a jihar Kwara, ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taron da ya yi da shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin jihar 16.

Ya ce taron sun gudanar da shi ne domin yin nazarin yadda zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya ya gudana, sai kuma tattauna yadda za a kara samun kuri’u masu dimbin yawa a zaben gwamna da na majalisar dokoki a ranar Asabar mai zuwa.

Lai ya ce jama’a su yi biris da duk wata barazana da masu adawa ke yi cewa za su hargitsa zaben a ranar Asabar mai zuwa.

Ya tabbatar musu da cewa gwamnati za ta samar da isassun jami’an tsaro wadanda za su kare dukiyoyin su da rakuyan su.

Lai ya ce ya samu labarin cewa ‘yan adawa na shirin yin amfani da ‘yan daba ta hanyar kai hari da firgita masu jefa kuri’a a lokacin da ake kan gudanar da zaben ranar Asabar mai zuwa.

“Mun samu labarin cewa za su dauko sojojin hayar ‘yan daba da wasu jihohi su shigo jihar Kwara domin su hargitsa zabe.

“To duk wanda ya kuskura ya aikata haka, ya sani cewa ya sadaukar da ran sa kawai.”

Jam’iyyar APC ce ta lashe zaben shugaban kasa da na sanatoci a jihar Kwara, inda aka kayar da Sanata Bukola Saraki, Shugaban Majalisar Dattawa.

Ta kuma lashe zaben majalisar tarayya daga kananan hukumomi shida.

Share.

game da Author