Hukumar Zabe ta dage zaben Adamawa

0

Hukumar Zabe ta dage zaben Adamawa da za ayi ranar Asabar mai zuwa.

Festus Okoye na hukumar ya bayyana cewa hukumar za ta bi umarnin kotu da ta ce a dakatar da zaben bisa kara da wani dan takara ya shigar cewa hukumar bata saka jam’iyyar sa ba a takardar kada kuri’a na gwamnan jihar.

Okoye ya ce INEC za ta daukaka kara domin a yi watsi da wannan kara da dan takarar ya shigar, don ta samu ta kammala zaben gwamna a jihar.

Idan ba a manta ba jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin da ba a kammala zaben gwamna ba.

A sakamakon zaben da aka bayyana bayan zaben jam’iyyar PDP ce ke kan gaba bisa yawan adadin kuri’un da aka kada a zaben.

Share.

game da Author