DALLA-DALLA: Hanyoyin Da INEC Za Ta Warware Kwatagwangwamar Zaben Ribas

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana dalla-dallar yadda za ta warware kwatagwangwamar da ta dabaibaye zaben gwamna a Jihar Ribas.

Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka, yau Alhamis a taron ganawa da manema labarai da INEC ta gudanar a hedikwatar ta, a Abuja.

Ya ce tsare-tsaren warware cukumurdar zaben ta fara ne tun a ranar 19 Ga Maris, ranar da INEC ta gana da dukkan masu hannu a sha’anin zaben Jihar Ribas.

Sai kuma ranar 29 Ga Maris, ranar da INEC ta gana da dukkan hukumomin da zaben Jihar Ribas ya shafa.

A ranar 30 Ga Maris kuma, har ila yau INEC za ta yi taro da masu takara da kuma shugabannin jam’iyya a jihar.

Daga nan ne kuma INEC za ta fito da Ka’idojin Ci Gaba da Tattara Sakamakon Zaben Jihar Ribas.

Tsakanin ranakun 25 zuwa 30 Ga Maris ne INEC za ta sake tantance masu sa-ido a zaben.

Za a yi wannan tantancewa ce a lokaci daya da Abuja da kuma can a Jihar Ribas.

Ranar 2 zuwa 5 Ga Afrilu ne INEC za ta ci gaba da tattara sakamakon zaben na Jihar Ribas.

An ware ranar 13 Ga Afrilu ta kasance ranar da za a sake yin zaben da bai kammalu ba, idan har hakan ta kasance bayan kammala tattara sakamakon zaben.

Za a bayyana sakamakon zabe da kuma wanda ya yi nasara a ranar 13 zuwa 15 Ga Afrilu.

Za a bayar da katin shaida ga wanda ya yi nasara, a ranar 19 Ga Afrilu.

Share.

game da Author