Dakarun hadin guiwa na sojojin dake fafatawa da Boko haram sun kashe wani jigon Boko Haram mai suna Malloum Moussa da mayakan sa 15 a tsibirin tekun Chadi.
Kakakin wannan runduna na sojoji, Timothy Antigha, ya bayyana cewa bayan ragargaza wadannan yan boko haram din da suka yi sun fatattaka motocin yaki biyar mallakar Boko Haram din.
Moussa, shine gogan da ke da iko a iyakokin Daban Masara, Kirta Wulgo da Koleram. Shi ne ke karbar haraji a wajen manoma da masu zama a wadannan garuruwa.