Ni a matsayina na karamin dalibin kimiyar siyasa nafi ganin kyakykyawar alakar hukumar zabe da kotu fiye da fadar shugaban kasa tunda ita hukuma ce mai ‘yanci. A tsarin yadda aikinta yake dole wannan ‘adjective’ din na harshen turanci wanda yake tare da sunan hukumar shine ya bata kariya wato ‘Independent’.
A tsarin siyasar gaskiya ana tabbatar da ‘yancin hukumar ne a cikin aiki ba wai kawai a suna ba. Misali, babu inda shugaban kasa zai soke zabe ko ya kwace nasarar wani don ya bawa wani. Amma kotu tana da ikon yin haka, wannan ai ya zama ruwan dare a Najeriya, ko a zaben Bauchi mun ga haka.
Shine yasa duk sanda akace gwamnati tana da iko akan hukumar zabe dole za a samu karkacewa a cikin aikinta shiyasa na kalubalanci hanyoyin samun kudin kungiyar da kuma samar da shugabancinta.
Duk sanda aka ce shugaban kasa ne zai na’da shugaban hukumar da kuma hanyoyin da take samun kudi, to babu shakka babu maganar ‘yanci a tare da hukumar.
Misali, lokacin da Umaru ‘Yar adua ya kafa kwamati na gyaran zaben Najeriya a karkashin jagorancin Justice Muhammad Lawan Uwais, daga cikin ‘recommendations’ din da kwamatin ya bayar har da tambaya akan ‘administrative autonomy’ (‘Yancin gudanarwa) na hukumar.
Yakamata ace hukumar zabe da kotu sun fi kowa karfi a Najeriya saboda dukkansu suna aiki da doka wacce ta basu ‘yanci. Duk sanda aka samu ‘independent judiciary and electoral body’ to gaskiya akwai cikakkiyar aiki da doka wacce zata samar wa wannan alqaryar cigaba.
Rashin hakan ne yasa ake samun matsaloli a kasashenmu, domin babu abun da yake tonawa Najeriya assiri kamar zabe da shari’a a kotu. Idan kotu ta lalace, hukumar zabe ta zama ‘partial’ to gaskiya an shiga uku saboda za a dinga zalunci, karan-tsaye, mulkin mallaka da kuma magudin zabe.
Shiyasa duk shugaban da yake yin aiki da doka babu ruwansa da shiga aikin INEC da kotu. Wannan shine abun da ya faru lokacin marigayi Umaru Musa Yar adua, duk da ya kalubalanci zaben da ya samar dashi a matsayin shugaban kasa amma kuma bai sauka daga mulkin ba an sake wani zaben saboda ba aikinsa bane sai kotu idan an kai mata kara gabanta.
Lokacin da wasu gwamnonin APC zasu fadi zabe babu abun da Buhari yace musu fiye da cewa, idan har suna zargin an musu magudi su tafi kotu duk da cewa hakan bai hanashi shiga cikin zargi ba a zaben wasu jihohin.
Allah ya shiryar damu.