Yari ya yi wa Allah laifi da ya ce APC ta yi zaben fidda-gwani a Zamfara, yayi gaggawan neman gafara – Marafa

0

Sanata mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Marafa, ya ce Gwamna Abdulaziz Yari ya yi sabon Allah, bisa karyar da ya tabka cewa wai jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda-gwani a Zamfara.

Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa dangane da dambarwar siyasar Zamfara, Marafa yace Yari ne ya haddasa dukkan rikicin da ya yi sanadiyyar INEC ta hana APC shiga zabe a Zamfara wanda daga baya kotu ta bata damar shiga zaben.

Daga nan sai ya jinjina wa Kotun Daukaka Kara saboda abin da ya kira, “hukunci mai adalci” da ya ce ta yanke a kan Zamfara.

Ranar 25 Ga Maris ne Kotun Daukaka Kara ta ce ta soke dukkan ‘yan takarar APC wadanda aka yi ikirarin su ne suka ci zaben Gwamna, Majalisar Dattawa da ta Tarayya da ta Jiha.

“Alkawarin Allah ne da ya ce ba zai taba goyon bayan rashin adalci ba.”

“Ina da tabbacin cewa kusan dukkan ku a nan, ana biyan ku a karshen ko wane wata, ba daga farkon wata ba. Don haka ina da tabbacin a karshen wannan rudanin, gaskiya za ta yi halin ta.

“Saboda Allah da Mala’iku ma sun san cewa ba a yi zaben fidda gwani a Zamfara ba, kamar yadda Yari ke cewa an yi. Kai kowa ma ya san cewa ba a yi zaben ba.

“Na karanta hukuncin da kotun ta yanke. Babu son zuciya, an yi adalci, haka ya kamata, ba kamar yadda Kotun Jiha ta yanke birkitaccen hukunci ba.”

Duk da Marafa ya ce Yari ya kunyata al’ummar Zamfara, ya roki Allah ya yafe masa.

Ya ce abin takaici ne shugaba kamar na Zamfara, inda ake ikirari da shari’ar Musulunci, ya fito ya kantara wa duniya karya.

Ya ce irin wannan shugaba addu’ar neman gafara a wajen Allah ya kamata a nemar masa, domin kada ya hadu da fushin Allah.

Daga nan sai ya ce wanda bai amince da hukuncin Kotun Dauakaka Kara ba, sai ya tafi mataki na karshe, wato Kotun Koli.

Shi ma Kakakin INEC, Festus Okoye cewa yayi Kotun Koli ce kadai za ta iya yanke hukuncin Zamfara a halin yanzu.

Tuni dai INEC ta dakatar da bai wa zababben gwamna da sauran zababbu daga jihar cewa ba za ta ba su takaidur shaidar lashe zabe ba, tun da Kotun Koli ta rage idan har ma wadanda aka hana din sun yanke shawarar kara daga kara zuwa Kotun Koli.

Share.

game da Author