An ragargaza kayan zabe a Jihar Benuwai

0

A Jihar Benuwai, an kai wa motocin daukar kayan zabe hari. Al’amarin ya faru ne a lokacin da motocin ke dauke da kayan zabe, a kan hanyar su ta kai kayan a Karamar Hukumar Ukem.

An tare motocin a kan hanyar Zaki Biam, a lokacin da suke dauke da kayan Mazabar Azendeshi.

An kuma ji wa wasu masu rakiyar kayan zaben rauni. Cikin wadanda aka ji wa rauni, har da Daniel Pila, wanda ya tabbatar da kai musu harin.

Shi ma Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Yilwatda, ya tabbatar da kai wa kayan zaben da jami’ai masu rakiyar kayan hari.

A jihar Benuwai dai za a sake zabe a wasu yankuna cikin Kananan Hukumomi 22.

Gwamna Samuel Ortom na PDP ya ba Emmanuel Jime na APC ratar kuri’u 81, 554.

Ortom ya na da 410,576, shi kuma Jime ya na da 329,022. Mutane 121,299 za su yi zaben.

Share.

game da Author