Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke kwamishinan Ayyuka na musamman na jihar Kano, Mukhtar Yakasai.
‘Yan sandan sun kama Yakasai ne a daidai ya na kokarin tarwatsa zabe a rumfunar zabe da ke karamar Hukumar Dala.
Tare da Yakasai akwai wasu gungun yan taratsi da ya jagoranta zuwa wadannan mazabu, duk an tarkata su zuwa caji ofis.