An kori karuwai fata-fata daga Umuahia, babban birnin Jihar Abia

0

Karuwan da ke yawon-ta-zubas a Umuahia, babban birnin Jihar Abia, sun shiga wasan buya, tun daga lokacin da gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin kakkabe karuwai daga titinan birnin tare kuma da kulle gidajen karuwan da ke Umuahia.

Wakilin da ya kewaya cikin birnin domin ganin ko kora da kamen karuwan na yin wani tasiri, ya ruwaito cewa a halin yanzu karuwai a birnin Umuahia sun a zaman dar-dar ne.

A ranar Litinin da ta gabata ne dai Gwamna Okezie Ikpeazu ya bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen karuwan da cikin birnin, musamman wadanda ke a kan Titin Orlu, Kaduna da na kan titin Arochukwu da sauran su.

Daga nan kuma Gwamna Ikpeazu ya bada umarnin gurfanar da masu gidajen da suka ajiye karuwan su na kwana zaman haya a ciki.

Ya kara da umartar a gurfanar da masu wuraren da suka bari ana tu’ammali da kuma shan haramtattun kwayoyi a cikin wuraren su.

Gwamnatin jihar dai ta ce gidajen karuwai da matattarar masu sha da sayar da kwayoyi sun zama mabuyar batagari da masu aikata muggan laifuka a jihar.

Ta ce daga nan suke kulla aika-aikar fita yin fashi da makami, kuma a can suke boyewa bayan sun gama tabka barnar su, musamman a cikin dare.

Share.

game da Author