Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da rokon da dan takarar gwamnan Jihar Ribas na jam’iyyar AAC ya yi mata, inda ya nemi ta haka INEC bayyana sakamakon zaben gwamna na jihar.
Dann takarar AAC ne, Biokpomabo Awara, wanda jam’iyyar APC bangaren Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi suka mara wa baya a zaben gwamna, shi ne ya shigar da wannan korafi a gaban koru, amma aka yi wasti da korafin na sa.
APC bangaren Amaechi ta mara masa baya, kwana uku kafin zabe.
Hakan ya biyo bayan haramcin da Kotun Koli ta yi wa jam’iyyar APC Reshen Jihar Ribas shiga takarar zaben gwamna, majalisar Tarayya da na majalisar dattawa da kuma na majalisar dokokin jihar.
Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ki amincewa da rokon da AAC ta yi.
Da farko INEC ta dakatar da bayyana sakamakon zaben jihar, saboda tashe-tashen hankula a lokaci da kuma bayan zabe.
Ta kara da cewa sojoji da ‘yan jagaliya sun dagula zaben.
Daga baya ta ce ta na da kwafen alkaluman sakamakon zaben na kananan hukumomi 17 daga cikin 23, wadanda aka rigaya aka kammala tattara sakamakon su.