Dan takarar jam’iyyar PDP Atiku abubakar, ya yi ikirarin cewa yayi nasara a wasu jihohi, wadanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari na APC ya yi nasara a can.
Haka Atiku ya bayyana a cikin takardar karar da ya shigar a Kotun Daukaka Kasa, wadda ke dauke da shafuka 139.
Ya bayyana dalla-dallar kididdigar sakamakon da ya ce shi ne ya samu na hakika, kamar yadda rumbun na’urar ajiyar sakamakon zaben INEC ya bayyana, kafin daga bisani a baddala sakamakon.
yace shi ne yay i nasara a jihohin Kogi, Kaduna, Gombe da Neja, amma daga baya duk aka bayyana APC ta yi nasara.
Ranar 27 Ga Fabrairu, INEC ta bayyana cewa Buhari na jam’iyyar APC ya samun kuri’u 15,191,847, shi kuma Atiku na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 11,262,978.
Sakamakon zaben ya nuna akwai ratar kuri’u 3,928,869 a tsakanin Buhari da Atiku.
Atiku y ace ya samu kuri’u 18,356,732, shi kuma Buhari ya samu 16,741,430.
Ya ce ya shiga gaban Buhari da yawan kuri’u 1,615,302 a na sa ikirarin.
Sannan kuma y ace yay i nasara a jihohi 21, banda Jihar Ribas wadda a lokacin ba a kammala kirga kuri’un ta ba.
Ya ce haka na’urar INEC ta nuna ya zuwa ranar 25 Ga Fabrairu, 2019.
Atiku ya ce jihohi 15 kawai Buhari ya ci.
INEC ta ce jihohin da Buhari y ace su ne: Bauchi, Borno, Ekiti, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Osun, Sokoto, Yobe da kuma Zamfara.
Atiku shi kuma ya samu nasara a jihohin Abia in Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Imo, Ondo, Oyo, Plateau, Rivers, Taraba and the FCT.
SAKAMAKON DA INEC TA FITAR
Kogi
Buhari: 285,894
Abubakar: 218,207
Jami’in Sakamakon Zabe, Michael Adikwu
Gombe
Buhari: 403,961
Abubakar: 138,484
Jami’in Sakamakon Zabe, Kyari Mohammed.
Kaduna
Buhari: 993,445
Abubakar: 649,612.
Jami’in Sakamakon Zabe, Bello Shehu
Neja
Abubakar: 218,052
Buhari: 612,371
Jami’in Sakamakon Zabe, Angela Mary
IKIRARIN ATIKU ABUBAKAR
Kogi
Mr Abubakar: 504,308
Mr Buhari: 431,479
Gombe
Abubakar: 684,077
Buhari: 115,225
Kaduna
Abubakar: 961,143
Buhari: 469,002
Neja
Abubakar: 576,308
Buhari: 504,218
A cikin karar da ya shigar, Atiku Abubakar ya bayyana dalilan sa da ya ce a soke sunan Buhari, a bayyana shi Atiku din a matsayin wanda yayi nasara, ko kuma gaba daya a soke zaben.
Discussion about this post