Bisa dukkan alamu murnar da kungiyar Ajax ke yi don ta kori Real Madrid daga gasar, ta koma ciki, ganin cewa da kungiyar Juvestus za ta kara a zagaye na uku na gasar.
Wannan kafasa da za su yi, tamkar maimata kafsawar su ce a wasan karshe cikin 1996. Duk da ana ganin Ajax ta yi sa’a a kan Madrid, a wannan karo, gida za a kora su a guje.
Ajax yaran kociya Erik ten Haag, kanana ne kwarai. Duk da dai an ce na kawo karfi ya fi an girme ni, to a wannan hadi da aka yi wa Ajax da Juventus, lallai baya ga grime musu da aka yi da manyan ‘yan wasa, irin su Ronaldo, Mandzukik da sauran su, to kuma an fi su karfin.
Yaran Ajax irin su Frenkie de Jong da Matthiji de Tadic ba za su iya cin kasuwa a tsakiyar masu tsaron gidan Juventus ba.
Duniya kuwa ta shaida, matsawar Ronaldo ya darzaza a cikin bayan Ajax, to babu waigin da zai iya tsaida shi. A tambayi Atletico Madrid a sha labari.
Wasan Ajax da Juventus ba zai taba hana kociyan Juvi, Massimilano Allegri barci ba, ko kadan.