Ranar cutar koda: Muna kira ga gwamnati kan a rage farashin kula da masu cutar -Kwararru

0

Wasu kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta rage farashin samun kula da mutanen dake fama da cutar koda keyi cewa tsadar kudin magani yayi yawa.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun yi wannan kira ne a ranar cutar Koda ta duniya ta hanyar wayar da wa mutane kai game da cutar da hanyoyin da za su bi don samun kariya daga kamuwa da cutar ganin cewa cutar na daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya.

Yawan shan magunguna,shan gida, busa taba sigari, rashin motsa jiki, kiba, rashin magance cutar hawan jini, zazzabin cizon sauro, kanjamau da sauran su na daga cikin ababen dake haddasa wannan cuta a jikin mutum.

Sannan alamomin cutar sun hada da yawan yin ciwon kai, kumburin jiki musamman kafafuwa,ciwon ciki da sauran su.

Wani mutum da ya yi fama da wannan cutar mai suna Femi Ibitokun ya bayyana cewa babban abin da zai taimaka wa masu fama da wannan cuta shine idan ana sama musu tallafi domin iya siyan magani.

Hanyoyi 8 da ya kamata ka sani game da cutar koda:

1. Ana iya gadon cutar koda daga wajen iyaye.

2. Yawan shan magunguna musamman ba tare da izinin likita ba na kawo cutar.

3. Kamuwa da cutar sanyi na kowo cutar.

4. Samun rauni a koda na kawo cutar.

5. Rashin shan maganin kawar da cutar hawan jini, zazzabin cizon sauro, kanjamau duk na iya kawo cutar.

6. Rashin motsa jiki da cin kayan abincin dake inganta kiwon lafiya na sa a kamu da cutar.

7. Zuwa asibiti domin yin gwajin cutar na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

8. Rage yawan cin gishiri musamman danyen gishiri a abinci na taimakawa wajen guje wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author