Rabon da wadannan manyan kungoyoyi su hadu a wasan siri-daya-kwale na Champions League, tun cikin kakar 200/2008, a wasan kusa da na karshe, inda Manchester ta yi nasara a kan Barcelona. Daga nan ne ta matsa gaba, ta yi nasarar cin kofin a karo na uku.
Tun daga nan kuwa Barcelona ta yi nasara a kan Man U sau biyu a wasan kusa da na karshe, cikin 2009 da kuma 2011. Ko a wannan karawa da za su yi a wannan gasa nan gaba kadan, ana sa ran cewa Barca ce za ta yi nasara a kan Man U.
Babban aikin da ke gaban ’yan bayan Man U shi ne su tabbatar da sun tsaida Leonel Messi, sun hana shi rawar gaban hantsi.
Wannan kuwa shi ne jan-aikin da ke gaban kociyan Man U, Ole Gunnar Solskjaer, wanda tsohon dan wasan kungiyar ne, kuma shi ne ya ci kwallon da ya bai wa Man U din nasarar daukar Kofin cikin 1999, a karawar su ta karshe da Bayern Munich.
Man U na da matsala, duk da nasarar da ta rika samu bagatatan tun bayan korar Jose Mourinho aka kawo Gunner, rashin nasarar da kungiyar ta samu sau biyu a jere a hannun Arsenal da kuma jiya Asarar a hannun Wolves, inda aka fitar da ita daga FA, ya nuna cewa ko da taron dangi ba za ta iya kwatar kan ta a hannun Barcelona ba.
Karfin su ba daya ba, gogewa ba daya ba, haka kuma matsalar da ke damun Man U ta fi ta Barca.
Barca dai ita ke tashe a yanzu, tun bayan korar Madrid daga gasar. Man U kuwa ba ta takama da komai sai tarihin baya.
Discussion about this post