Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta kama wasu masu aikata miyagun aiyukka 52 daga ranar 6 zuwa 11 ga watan Maris a jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan Hakeem Busari ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a Lokoja inda ya kara da cewa masu sace akwatunan zabe,’yan jagaliya da masu rike da makamai ba tare da izinin yin haka ba na cikin mutanen da suka kama a ranar zabe.
Segun Olu, Yakubu Zakari, Salifu Mohammed Ajeshola Michael, Sabiu Halidu, Adamu Idris, Ojoma Eugene, Sunday Abu, Isaac Edoh, Joshua Ejibo, Ojogo Alhaji da Monday Amodu na cikin wadanda ‘yan sandan suka kama ranar zabe.
Busari yace sun kama Segu Olu da laifin harbe ma’aikacin hukumar zabe da wani cikin mutanen da suka zo kada kuri’a a kauyen Egbe dake karamar hukumar Yagba ta Yamma sannan sun kama sauran ‘yan jagaliyar ne a garin Ibaji da wasu sassan yankin.
” Mun kama su dauke da makamai dabam-dabam.
Bayan haka Busari ya kara da cewa rundunar ta kama wasu mutane 40 da laifin satar shanu, fashi da makami da garkuwa da mutane.
Musa Haruna, Haruna Ahmadu, Ibrahim Haruna, Gambo Dauda da Sani Yunusa na daga cikin masu garkuwa da mutane da rundunar ta kama.
Busari yace rundunar ta gano cewa wadannan mutanen ne suka yi garkuwa da wani Usman Magaji a kauyen Adogo dake karamar hukumar Ajaokuta ranar 7 ga watan Janairu inda bayan sun tsare shi na dan wani lokaci suka kashe shi.
A karshe Busari yace sun kama sauran masu garkuwa da mutane da masu fashi da makami a garuruwan Ganaja, Gegu Beki da Koton Karfe dauke da bindigogi, harsashai, mota daya, wayoyin hannu da adduna.
Discussion about this post