ZABE: Mutane miliyan 72 su ka karbi katin rajistar su, inji INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ce ya zuwa ranar rufe karbar katin zabe, ‘yan Najeriya miliyan 72,775,565 ne suka karbi katin zaben su a hannu.

Hakan ya yi nuni da cewa jimillar kuri’un da za a jefa a ranar Asabar mai zuwa ba za su wuce miliyan 72,775,585 ba kenan.

Domin babu wanda za a amince ya jefa kuri’a sai wanda ya yanki katin rajistar yin zabe.

Sannan kuma INEC ta ce yawan katin zabe da ba a karba ba, sun kai miliyan 11,228,582.

Hakan kuma na nuni da cewa duk wanda ya yi rajista amma bai je ya karbi katin sa ba, to ba za a bari ya yi zabe ba, ko ma wane ne.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana cewa mutane milyan 84 ke da rajitar zabe a hannun su.

INEC ta yi alkawarin buga adadin yawan katin zaben da ba a karba ba har yanzu.

Tun a ranar 11 Ga Fabrairu ne INEC ta rufe kofar karbar katin zabe ga wanda bai karba ba tun tuni.

Ya ce dukkan katin zaben da ba a karba ba, an adana su a Babban Bankin Najeriya, CBN, sai bayan an kammala zabe sannan INEC za ta karbo su ta ci gaba da raba wa masu su.

Share.

game da Author