Masu garkuwa sun sace dan wani limamin coci a jihar Filato

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Tyopev Terna ya bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace dan wani limamin cocin dake kwalejin kimiya dake karamin hukumar Barkin Ladi a jihar Filato.

Terna ya ce limamin cocin kuma mahaifin yaron Andrew Dido ya kawo karar sace dan nasa a ofishin su ranar Alhamis.

” Andrew ya ce masu garkuwan sun far wa gidansa da karfe tara na daren Laraba sannan suka tafi da dansa mai suna Kim Dido mai shekaru 12. Sun kwace wayar dake hannun sa sannan suka bar lambar wayar da za a iya kiransu da shi kamar haka 0803644144.”

Terna ya ce bayan sun samu wannan rahoto sai suka tura jami’an su domin bin dazukan dake kewaye da su domin kamo masu garkuwan a inda suka boye yaron sannan a ceto sa.

Ya kuma ce sun saka jami’an tsaro a wannan makaranta domin samar da tsaro sannan sun yi kira ga mutane da su gaggauta tuntubar jami’an tsaro idan a ka samu bayanan da zai iya taimakawa wajen ceto wannan yaron.

Share.

game da Author