Ba zan yi murabus ba daga shugabancin Hukumar Zabe – Mahmood Yakubu

0

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa ba zai you murabus ba kamar yadda wasu ke Kira da yayi.

Mahmood ya ce idan da ko akwai dalilin yin murabus din ko tantama ba zai yi ba, zai mika takardar sa ya Kara gaba.

” Bana cikin takura ko matsi a hukumar da zai sa in ajiye aiki na. Amma fa idan da akwai dalili, ko tantama ba zan yi ba, zan karkade takalma na in ajiye musu aikin su in Kara gaba. Akwai aikin da muka sa a gaba yanzu a hukumar na tabbatar da anyi Zaben dake gaba kamar yadda aka shirya.

Sai dai Kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da zarar an Kammala zabukan dake gaba, zai bi diddigin musabbabin dage Zabe da aka yi a Kwanakin baya.

Wannan furuci da yayi ya kawo cecekuce a kasa Inda wasu ke ganin shugaba Buhari ya riga ya ya san da cewa shine zai lashe zaben dake tafe.

Share.

game da Author