Mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Barnabas Bala Bantex ya sha kasa a zaben sanata Kaduna ta Kudu.
Sanata Danjuma Laah na jam’iyyar PDP ne ya lashe zaben da kuri’u 268,923, inda Bantex ya tashi da Kuri’u 133,287.
Idan ba a manta ba Bantex ya hakura da ci gaba da zama mataimakin gwamnan jihar Kaduna inda ya roki gwamnan ya barshi ya koma yankin Kaduna ta Kudu domin takarar kujerar Sanata.
Tuni har gwamnan El-Rufai ya musanya shi da Hajiya Hadiza Baklarabe.