Sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani, ya yi kira ga hukumar Zabe da ta gaggauta soke zaben Kaduna cewa ba a yi zaben arziki ba.
Shehu Sani ya bayyana haka ne a taron manema labarai da yayi a garin Kaduna ranar Litinin.
A wajen taron Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa an yi ta yin murdiya a wurare da yawa a fadin jihar da ya yi dalilin nasarar da wasu suka samu.
” An yi ta yin aringizon kuri’u a wurare da dama sannan a wasu kananan hukumomin jihar, kamar Igabi, canja ma’aikatan zabe a aka yi a ranar zaben. Sannan A Birnin Gwari ma da karfin tsiya ke tursasa wa ma’aikata da masu zabe.
” A karamar hukumar Igabi kuwa, kawai rubuta kuri’un boge aka rika yi. Sannan Kuma an ki kai wa mutanen dake kudancin kaduna kayan aiki da wuri sai kusan da karfe 7 na yamma amma kuma an kai wa wasu akan lokaci.
Shehu Sani ya ce idan har hukumar zabe bata ce wani abu akai ba da wuri-wuri, jam’iyyar sa ta PRP za ata garzaya kotu domin a bi mata hakkin ta.