Fitacciyar ‘yar siyasa, Binta Masi dake wakiltar Adamawa ta Arewa ta sha kaye a zaben wannan kujera da take sake nema a zaben da aka yi ranar Asabar.
A sakamakon zaben da Mamman Baba-Ardo na hukumar zabe ya sanar Ishaku Cliff na jam’iyyar PDP da kuri’u 43,117 ya lashe zaben.
Binta na Jam’iyyar APC ta samu kuri’u 16,219.