Kotu ta tsige dan takarar APC na gwamnan Enugu

0

Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta tsige Ayogu Eze daga takarar gwamnan jihar Enugu, ta maye gurbin sa da George Ogara.

Mai Shari’a Inyang Ekwo, ya umarci INEC ta cire sunan Eze daga jerin masu takara ta maida sunan George Ogara a madadin sa.

Mai Shari’a ya ce saboda Ogara ne ya fi samunn yawan kuri’un da aka jefa a kananan hukumomi 17 na cikin jihar.

Ogara ne ya shigar da karar Shugaban APC na Kasa, Adams Oshiomhole, Moses Momoh da kuma INEC, inda ya kalubalanci sakamakon zaben da su Oshiomhole suka bai wa INEC cewa Eze ne ya yi nasara, ba shi ba.

Mai Shari’a ya ce Ogara ne halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar APC na Jihar Enugu, domin shi ne ya yi nasara a bisa sharuddan zaben dan takarar fidda gwani kamar yadda dokar zabe ta kasa da kuma ta jam’iyyar APC suka gindaya.

Sai dai kuma har yanzu Eze bai hakura ba, ya ce sai ya bi hakkin sa a Kotun Daukaka Kasa, domin shi ne halastacce.

Jam’iyyar APC ta shiga rudu a jihohi da dama tunnbayan zaben fidda gwani da ta gudanar wanda aka sha fama da magudi a fadin kasar nan.
Jihar Rivers, Zamfara, Imo, Enugu da sauran jihohi da dama na cikin wannan tsomomuwar.

Share.

game da Author