Gwamnatin Tarayya ta ce kafin karshen 2019 za ta hana shigo da tumatir na gwangwani da na cikin leda a kasar nan. Ministan Harkokin Noma, Audu Ogbe ne ya bayyana haka.
Ya yi wannan jawabin ne a ziyarar da ya kai masana’antar markada tumatir da ke Kadawa, a Kano, jiya Talata.
Rahoton da The Cable ta ruwaito ya nuna cewa Ogbe ya hakkake cewa hana shigo da tumatir din na gwamwani da na leda zai taimaka wajen sarrafa markadadden sa a nan Najeriya.
“Gwamnatin Tarayya ta ware naira biliyan 250 domin bai wa manoman tumatir lamunin inganta noman tumatir. Za a ba su wannan lamunin ne a karkashin shirin Babban Bankin Najeriya CBN da kuma Bankin Manoma, wato Anchor Borrower Scheme.”
Ministan ya yi karin haske da cewa gwamnatin tarayya za ta yi iyakar kokarin ta domin tallafa wa masana’antun inganta harkokin noma na Dangote da kuma manona domin inganta noma da sarrafa tumatir a Najeriya.
Ya ce abin haushi ne ganin rahoton irin yadda aka ce ana kashe dala biliyan 22 a duk shekara wajen shigo da tumatir na gwangwani a cikin kasar nan.
Minista ya ce manoma za su rika noma tumatir su na sayar wa masana’antar sarrafa tumatir irin ta Dangote.
Sai dai kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile, wanda ya halarci Kadawa shi ma, ya bayyana cewa CBN ce ta bai wa kamfanin Dangote tallafin lamuni na naira bilyan daya da milyan dari uku domin rika noma tumatir din da za a rika sarrafawa.
Ya ce an shigo da tsarin Green House, wanda za a samar da irin tumatir har kwara miliyan 3 ga manoma.
Godwin Emefile ya ce wannan irin zai rika samar da tan 70,000 na tumatir a kowace hekta daya, maimakon wanda a baya can manoman ke shukawa su na samun tan 10,000 kacal a kowace hekta.