‘Yar takarar shugabanci kasa, kuma mace matsashiya mai suna Eunice Atuejide, ta bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da isasshen kuzarin iya ci gaba da mulkin Najeriya a zabe mai zuwa.
Eunice wadda ke takara a karkashin jam’iyyar da ta kafa da kan ta, ta ce za ta bi hakki a shari’ance cewa ko da Buhari ya zama shugaban kasa a zabe mai zuwa, to zagurfanar da shi a kotu tare da tulin hujjojin da za su sa a haramta masa shugabancin, domin ba zai iya ba.
Eunice mai shekara 39, ta ce za su maka Buhari kara kafin a gudanar da zabe, saboda haka ko da bayan ya yi nasara ne, za a iya dakatar da shi daga zarvewa a kan mulki.
PREMIUM TIMES ta yi hira da Eunice kwanaki kadan kafin gamayyar jam’iyyun siyasa, wato CUPP ta fitar da sanarwar cewa Buhari ba zai iya ba.
Ta ce sun yanke shawarar maka Buhari kotu domin a hana shi ci gaba da mulki ne, tunda ya rika kalamai na soki-burutsu a wurin kamfen da kuma wata faduwa da kusa a lokacin da ya yi kokarin zaunawa a wurin wani kamfen.
Tuni dai jaridar Punch ta buga labarin cewa an rigaya an shigar da karar.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta maida wa Eunice martani cewa Buhari lafiya garau ya ke, zai iya ci gaba da mulki domin babu abin da ke damun sa.