Cin Zogale ga mace mai ciki na yi wa jaririn dake cikin illa matuka – Bincike

0

Kamar yadda aka sani ne cewa zogale ganye ne dake dauke da sinadarorin dake samar wa mai ci lafiya da kuma kare shi daga kamuwa da cututtuka, hakan bai hana binciko wasu illoli da ke tattare da cin shi ba musamman ga mata masu ciki.

Ganyen Zogale na taimaka wa wajen kawar da hawan jini, cututtukan dake kama zuciya, ciwon siga, cutar daji, inganta fatar mutum da dai sauran su.

Sai dai duk da wannan amfani da Zogale keyi wasu likitoci daga jami’ar Ibadan sun yi kira ga mata masu ciki da su nesanta kan su daga cin ganyen Zogale, ‘ya’yan Zogale da man Zogale domin yana yi wa dan dake ciki illa.

Prof. Adefolarin Malomo, Foluso Atiba da Dr Innocent Imosemi ne suka gano haka a binciken da suka gudanar a jikin wasu beraye 20 dake dauke da ciki.

Sakamakon binciken ya nuna cewa ganyen Zogale na yi wa kwakwalwa, jijiyoyi da kasusuwan jaririn dake ciki illa matuka tun kafin ya zo duniya.

Malamo ya ce alamun illolin da Zogale ke yi wa jarirai sun hada da haifo dan da bashi da kafafuwa ko kunne ko baki ko cibiya sannan kuma da kasusuwa marasa karfi da dai sauran su.

Likitocin sun yi kira ga mata masu ciki da su hakura da cin ganyen Zogale a duk lokacin da suke dauke da ciki.

Share.

game da Author