Zolaya Buhari ya ke yi cewa da yayi wai ‘Ina son kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi’ – Kwamitin Kamfen

0

Darektan yada labarai na Kwamitin Kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari Festus Keyamo ya bayyana cewa ba daidai bane yadda ake ta yada wa wai ya yi kira ga mutanen Zamfara da su kwana da shirin ko ta kwana.

A ziyarar Kamfen da ya kai garin Gusau, Buhari ya ce ‘Ina son kowa ya cika cikin sa in ma fitinan ne aje ayi’.

Hakan bai yi wa mutane da dama dadi ba musamman ‘yan adawa inda suka rika cewa wannan magana bai dace ya fito daga bakin shugaban kasa ba.

Keyamo ya ce duka wanda ya san Buhari ya san mutum ne mai yawan barkwanci saboda haka ko a wancan lokacin da yake wannan bayani ya hada ne za zolaya ba wai da gaske yake yi ba.

” Abinda Buhari yake nufi shine ‘Irin yadda aka samu yalwa a noman shinkafa, mutane su tabbata sun dame cikin tam da tuwo saboda gujewa rudin shaidan kada su kai ga fadawa cikin fitintinun da babu gaira-babu dalili. Kuma ma dai Buhari ba’a ya ke yi.

” Muna kira ga dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da ya daina ruruta abin. Ya sani cewa Allah ke ba da mulki. Ya dai na ruruta abin kamar sama da kasa zasu hade. Ya sani cewa Najeriya ba ta siyarwa bace.

Share.

game da Author