Kamfanin Coverton Helicopter, masu bada hayar kananan jirage masu saukar ungulu, sun bayyana cewa rashin kyawon yanayi ne ya haddasa hatsarin da jirgin na su ya yi da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, jiya Asabar a Kabba, jihar Kogi.
Jirgin wanda samfurin Agusta Aw139 ne, ya fado daidai karfe 3 na yamma a lokacin da ya ke kokarin sauka kasa.
Haka Babban Jami’in kamfanin mai suna Josiah Choms ya bayyana.
Choms ya ce tuni sun sanar wa hukumar da alhakin gudanar da bincike ya shafa, kuma za a binciki musabbabin hatsarin.
Kakakin Yada Labaran Osinbajo, mai suna Laolu Akande, ya ce baya ga Mataimakin Shugaban Kasa, akwai Ministan Kwadago da wasu mutane 10 a cikin jirgin.
Tuni dai Osinbajo ya zarce zuwa wurin taron siyasar da je yi a Kabba.
Atiku Abubakar
Dan takarar shugaban kasa, a karkashin babbar jam’iyyar adawa, PDP, Atiku Abubakar na a sahun gaba na wadanda suka yi wa Osinbajo jajen hatsarin wanda ya ritsa da shi a cikin helikwafta na baya a Kabba.
Atiku ya garzaya shafin sa na twitter ya yi wa Osinbajo jaje da rokon Allah ya kiyaye na gaba.
Haka ita ma jam’iyyar PDP ta yi wa Osinbajo jaje da nuna alhini da kuma fatan kiyaye gaba.
A na sa bangaren, Osinbajo ya gode wa daukacin wadanda su ka taya shi jimami da yi masa jaje.
A cikin sanarwar da kakakin hada lanaran sa, Akande ya fitar, ya ce Osinbajo ya gode wa dimbin jama’a kuma tuni ya zarce ya ci gaba da gudanar da aikin da ya kai shi jihar Kogi din.
Bayannan kuma Babban limamin Cocin RCCG, Fasto Adeboye ya jagorancin taron ibada da addu’o’i na musamman domin Allah ya Kara kiyaye wa da yi wa Allah godiya ganin babu wanda ya sami Koda kwarzani a jikin sa cikin wadanda suke jirgin.