Ministan Harkokin Ilimi Adamu Adamu, ya bayyana damuwar sa dangane da yadda jami’o’i da yawa ke kauce hanya wajen kashe makudan kudaden da Gwamnatin Tarayya ke raba musu a kowace shekara.
Ya nuna wannan damuwar ce a taron da Ministan ya yi jiya Lahadi tare da ‘yan jaridu a Abuja.
A kan haka ne ya ce nan ba da dadewa ba za a kafa kwakkwaran kwamitin da zai rika bi kowace jami’a domin ya binciko bayanan yadda suka rika kashe kudaden da ya ce a ke narka musu a kowace shekara.
Duk da dai Adamu bai bayyana sunan jami’a ko daya ba Ga manema labarai, amma a cikin fushi ya yi bayani dalla-dalla tare da fayyace adadin da ya ce aka narka wa kowace jami’a.
Ba a kan jami’o’i kadai ministan na ilmi ya nuna damuwar sa ba. Har da Manyan Kwalejojin Fasaha da Manyan Kwalejojin Ilmi da ke fadin kasar nan.
Da ya ke ci gaba da fayyace wa, Adamu ya ce a cikin shekaru hudu Gwamnatin Tarayya ta raba wa manyan makarantun Ilmi na Jami’o’i naira bilyan 727.
Ya ce an raba musu wadannan kudaden ne daga Asusun Tallafa Wa Manyan Makarantu, wato TETFund.
“A cikin 2015 mun raba wa kowace jami’a daga jami’o’i 74 da mu ke da su, naira milyan 337 kowace. A 2016 kowace jami’a ta samu naira bilyan 1. Sannan cikin 2017 an raba wa kowace jami’a naira milyan 659.
” A shekarar 2018 da ta gabata kuwa an raba naira milyan 785 ga kowace jami’a.
Bai tsaya a nan, sai da Adamu ya ci gaba da lissafa dukkan adadin makudan kudaden da ya ce an narka wa Manyan Kwalejojin Fasaha da Manyan Kwalejojin Ilmi na kasar nan kakaf.
Discussion about this post