Babban Basaraken kasar Yarabawa, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi II, ya ce da abin bautar Yarabawa, wato Oluarogbo da Yesu Almasihu duk daya su ke.
Ya yi wa ‘yan jarida wannan bayanin ne a ganawar su jiya Asabar wurin bukin tunawa da ranar da Yarabawa su ka ce Oluarogbo ya tafi sama wajen Ubangiji.
An shirya kasaitaccen bikin ne a garin Ile-Ife inda fadar Ooni din ta ke.
Labaran kunne-ya-girmi-kaka da Yarabawa su ka yi imani da shi, sun nuna cewa mahaifiyar Oluarogbo ce ‘allolin’ Yarabawa su ka yi wa ishara cewa ta sadaukar da dan na ta, domin ya zama mai ceton Ile-Ife daga munanan hare-haren da su ka rika fuskanta daga kabilun Igbo.
An ce ta dauki dan na ta ta kai ta sadaukar ga wata ubangijiyar su da ke cikin ruwa.
Labarin ya ci gaba da cewa, amma maimakon Oluarogbo ya nutse a ruwa, wai sai ya yi sauri ya tubka igiya, ya rika taka ta, ya na yin sama, har ya kai inda ubangiji ya tattara mashahuran daular Ile-Ife da aka ce har yau su na can sama da ran su.
Ooni na Ife ya ce don haka misalin Oluarogbo kamar misalin Yesu Almasihu ne, wanda aka gicciye domin ya sadaukar da jinin sa wajen ceton Kiristoci a duniya.
Sai ya kara da cewa: “Kamar yadda Almasihu ya ke dan Allah, shi ma Oluagrobo dan Allah ne, domin an sadaukar da shi ne don ceton al’umma.”
Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa a daina yi wa Yarabawa kallon su na bautar gunki. Su na gunki ne su ke bauta ba.
Ya ce yadda Yesu ya ke da daya tilo a wajen mahaifiyar sa, Maryama, haka shi ma Oluarogbo ya kasance daya tilo a wajen mahaifiyar sa Moremi.