ZAMFARA: An dakatar da Hakimai biyu saboda zargin hulda da masu garkuwa, an kuma zargi ‘yan sanda

0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da wasu hakimai biyu saboda zargin su da hannu wajen goyon bayan ayyukan sace-sace a jihar Zamfara.

Wadanda aka dakatar din sun hada da Hakimin Kaya mai suna Bello Mai Wurno da ke cikin karamar hukumar Maradun, sai kuma Dangaladiman Birnin Magaji da ke cikin karamar hukumar Birnin Magaji.

Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu, Bello Gamji ne ya bayyana haka a Gusau, tare da cewa wadanda ake zargin su mika kan su ga dakarun NCDSC domin a bincike su.

Ya ce ana zargin su na kai wa barayin man fetur da kuma abinci.

Idan ba a manta ba, jihar Zamfara ta haramta wa kowa yin sana’ar bumburutu domin a takaita hare-haren makasa.
Kwamishinan ya ce abin ban-haushi shi ne wadannan hakimai sun bari ana saida mai a yankunan masarautun su.
Ya kara da cewa an kuma kama wasu da ake zargin su na taimaka wa maharan.

Daga nan ya zargi jami’an ‘yan sanda da bai wa gwamnati rahotannin karya dangane da halin da masu hari da garkuwa da mutane ke ciki.

“Mun gano kuma cewa wasu ‘yan sanda na ba mu bayanai na karya dangane da inda barayin nan suke. Daga baya sai muka gano duk karya suke yi mana, ba bayanai na gaskiya ba ne, saboda mun gano su na goyon bayan barayin domin su na amfana da su.” Inji kwamishinan.

Share.

game da Author